Shahararren dan wasan kwallon kafa na Brazil Pele, wanda ya shahara a duniya, da farko, a matsayin matashi mai cin kwallaye, wanda kuma ya jagoranci tawagar kasarsa ta lashe gasar cin kofin duniya har sau uku, wanda ba a taba yin haka ba, ya rasu jiya Alhamis yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.
An kwantar da shi a asibiti a karshen watan Nuwamban da ya wuce, kuma likitoci sun fada a watan nan na Disamba cewa yana fama da ciwon daji wanda ya karu tare da ciwon koda da zuciya. A watan Satumban 2021, an yi masa tiyata don cire masa wani kari daga hanjinsa.
Hukumar Asibitin Albert Einstein, inda aka yi jinyar Pele, ta fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ya mutu ne sakamakon raunuka a bangarorin jikinsa masu aiki.
‘Yar sa Kely Nascimento ta wallafa a shafinta na Instagram cewa “Duk abin da muke shi ne godiya gare ka, muna son ka har abada, Allah ya jikanka.”