Tana amfani da kwallo wajen yin zane-zanen da take karrama ‘yan wasa, kamar fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Brazil, Pele. Yayinda gasar cin Kofin Duniya ta dauki hankalin masu sha’awar kwallon kafa , wannan kuma ya karawa Lili Cantero kwarin guiwa, wadda ta ke amfani da zane- zane wajen nuna irin kyaun da wassan ya ke da shi.
Lili tana karrama kungiyoyin kwallon kafar da su ka ci Kofin Duniya ta wajen yin zane-zane kan kwallon a wajen gasar cin Kofin Duniya.
Lokacin da Cantero ta ji labarin rashin lafiyar dan fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Brazil Pele dan shekaru 82, sai ta tsaida shawarar amfani da baiwarta wajen karrama mutumin da aka dauka a matsayin wanda ya fi fice a fannin wasan kwallon kafa.
Cantero ta fara tunanin hada amfani da baiwar da take da ita a fannin wasanni, lokacin da abokanta su ka roke ta ta yi masu zane zane a takalman kwallon kafar su.
Kafa hoton takalmin da Cantero ta yi mashi zane a kai da Messi ya yi, ya karrade kafafen sada zumunta ya kuma dauki hankalin gwamnatin Paraguay da ya sa ta tura ta Qatar domin baje kollinta.
Banda zanen da ta karrama Pelé, an kuma baje kolin samfarin zane-zanen Cantero a dakin baje kolin kayan wasan kwallon kafa na kungiyar kwallon kafa ta Amurka a Doba, da ya hada da kwallayen da aka karrama fitattun ‘yan wasan kwallon kafa kamar zanen dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego Maradona.
Cantero ta bayyana cewa, ta dade tana mafarkin nuna baiwar ta a gasar cin Kofin Duniya, kuma kwalliyarta ta biya kudin sabulu, mafarkinta ya cika.