ABUJA, NIGERIA - Jim kadan bayan hukuncin kotun, kungiyar dattawan Arewa wato NEF, gwamnoni, masu fada a ji a harkokin yau da kullum da kuma ‘yan siyasa sun yi kira da kakkausar murya ga dukkan ‘yan kasa da su jajirce wajen zaben shuwagabanni a dukkan matakai masu nagarta da suka cancanta ba tare da yin la’akari da yanki ko addini ba domin kawo karshen rudanin da kasar ke ciki a halin yanzu ta fuskar matsaloli masu alaka da karancın sabbin takardun kudi, komadar tattalin arziki, kawo karshen talauci da matsalolin tsaro da kuma mafi mahimmanci a zabi shugaban kasa wanda zai rika sauraron koken al’umma da dai sauransu.
Masu ruwa da tsakin dai sun yi wannan kira ne jim kadan bayan da kotun koli ta dage karar da aka shigar domin kalubalanta da kuma kare manufar sauya fasalin Naira na babban bankin Najeriya wato CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki wanda zai yi daidai da kwanaki uku kacal kafin a gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.
Dakta Hakeem Baba-Ahmad, da ke zaman kakakin kungiyar dattawan Arewa ya bayyana matsayın kungiyarsu ta NEF jim kadan bayan dage sauraron karar da kotun koli ta yi.
Wannan al’amari dai ya zo daidai da taron cika shekaru 10 da kafuwar kungiyar dattawan Arewa wato NEF da aka gudanar a birnin tarayya Abuja inda akasarin mahalarta da suka kunshi masu ruwa da tsaki daga sassan Arewacin Najeriya daban-daban suka yi ta jaddada mahimmancin zaben shugawagabanni da suka cancanta, wadanda za su rika sauraron ‘yan kasa da kunnen basira don kawo karshen matsalolin da kasar ke fama da su da kuma ci gaba mai dorewa.
Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya bayyana rashin jin dadinsa a game da batun kin mutunta kara wa’adi na yin amfani da tsoffin takardun Naira 200, 500 da dubu 1 bayan dage sauraron karar da takwarorinsa na Kaduna, Zamfara da Kogi suka shigar a gaban kotun koli zuwa ranar 22 ga watan Febrairun.
Gwamnan yana mai cewa ‘yan kasa na cikin halin kakani-kayi ba sa iya gudanar da harkokin su na yau da kullum yadda suka saba kasancewar sun ci gaba da tafka asara ya na mai yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya duba wannan ala’amari don saukakawa ‘yan kasa radadin da suke ji.
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa kana darakta a fannin kulawa da harkoki a kungiyar NEF, Alhaji Nastura Ashir Sahriff, ya ce kotun koli ta dage sauraron karar da gwamnonin uku suka shigar a game da tsaffin takardun kudi ne saboda yadda shugaban kasa ya ki fitowa ya nuna cewa bankin CBN ya yi biyayya ga umarnin kotun.
A wani bangare kuma, a yayin taronsu na cika shekara 10 da kafuwa, dattawan arewa sun cimma matsayar cewa za su kada kuri'a daidai da bukatun ‘yan kasa da na kungiyarsu, zasu bada himma wajen tallafa wa batun gudanar da sahihin zabe da mika mulki cikin lumana zuwa zababben gwamnati mai zuwa, bijire wa duk wani yunkuri na murkushe tsarin dimokuradiyya ta kowace hanya da ta saba wa kundin tsarin mulkin kasa, mutunta ra'ayoyin al'ummar Najeriya ta hanyar ingantaccen zabe, ba tare da la'akari da asali da ko wanda ya yi nasara ba.
Sannan a goyi bayan gwamnati mai zuwa don magance manyan kalubalen da ke hana ci gaba da samun zaman lafiya, da kuma tsaro a Arewa da Najeriya baki daya.
Shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya bukaci yan kasa su yi hakuri a game da halin da ake ciki tare da cewa su fito zu zabi cancanta don kawar da zalunci da halin matsatsi da ake ciki.
Shi ma babban daraktan gudanarwar kungiyar NEF, Farfesa Dognang Sheni, ya bayyana cewa kamata ya yi ‘yan arewa su hada kai don a zabi mutumin da zai kawo ci gaba a yankinsu.
Ya zuwa yanzu dai, yan Najeriya na cikin rudani a game da tsoffin takardun kudinsu dake tattare da su ganin cewa irin matsayar kotun koli na yau Laraba.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: