ABUJA, NIGERIA - A yayin da al’ummar Najeriya ke dakon sakamokon hukuncin da kotun koli na kasar za ta zartar a zaman da za ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairu kan batun kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudaden da aka canja a kasar, wani batu da ke ci gaba da daukar hankali shi ne yadda 'yan kasuwa ke karya farashin kayyakinsu saboda karancin kudin da ake ci gaba da fama da shi, lamarin da masana ke gannin ka iya haifar da koma baya ga tattalin arzikin kasa.
Wannan al'amari ba za a kira shi da faduwar farashi ba sai dai wani kalubale na wucin gadi.
Da haka muka ji ta bakin wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum Hassan Sardauna, ko wane tasiri hakan ke da shi a kan mutane.
Su kansu da lamarin ya shafa kai tsaye, wato 'yan kasuwa, sun bayyana mana mabanbantan ra'ayoyi a kan wannan al'amari
Sannan kuma Dakta Isa Abdullahi, masanin tattalin arzikin kasa, ya yi mana tsokaci a kan tasirin da wannan batu ya yi ga tattalin arzikin 'yan kasuwa da na kasa baki daya, da kuma hasashen abinda zai faru nan gaba.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru da dama da al'ummar Najeriya ke tsintar kansu cikin tsaka mai wuya sakamakon canjin kudin Naira, al'amarin da tuni masana, masu ruwa da tsaki, 'yan kasuwa, da kuma magidanta ke kira a kai, a sake lale a kan batun, domin ceto kasar daga halin matsin da take ciki a halin yanzu.
Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: