Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kin Bin Umarnin Kotu Kan Batun Sabon Kudi Zai Iya Yamutsa Najeriya - Masana


Buhari da Emefiela Rike da Sabuwar Takardar Naira
Buhari da Emefiela Rike da Sabuwar Takardar Naira

Wasu masu ruwa da tsaki na gargadi kan rudamin da ka iya biyo bayan watsi da umurnin tsawaita lokacin cikar wa'adin daina amfani da tsoffin takardun naira.

Biyo bayan kalaman gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, wanda ya ce wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, 500 da dubu 1 na nan daram, masana shari’a da sauran masu ruwa da tsaki a kasar sun ce kin bin umarnin kotu da ya baiwa ‘yan kasa damar su ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har sai kotun ta yanke hukunci a kan lamarin, zai iya kawo yamutsi a kasar.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana wannan matsaya na babu gudu ba ja da baya a game da daina amafani da tsoffin takardun kudin ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke birnin Tarayya Abuja a ranar Talata

Emefiele ya ce an fara samun sauki a al’amarin karancin sabbin takardun kudi sosai tun lokacin da aka fara biyan kuɗaɗen a cikin bankuna wato over the counter payment baya ga samu a nau’urar ATM da kuma amfani da manyan wakilan babban bankin kasar, yana mai cewa don haka babu bukatar yin la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu.

Bayanin na Emefiele na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasa ke cikin rudami a game da umarnin kotun kolin da ta tsawaita wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu har zuwa ga lokacin da kotun zata yi sauraron karar da gwamnonin uku daga arewacin kasar suka shigar a gabanta.

Shin menene tanadin doka idan aka samu irin wannan sabani da ake gani inda bankin CBN ya ce ba zai sauya matsaya ba duk da umarnin kotun koli, Barrista Mainasa Kogo ya ce kememe da gwamna Emefiele ya yi da kuma kin bin umarnin kotu zai iya kawo yamutsi a kasa kasancewa al’umma na cikin halin kakani-kayi.

Mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Baba Yusuf, ya bayyana cewa kememe da gwamna Emefiele ya yi ba laifin sa ba ne illa ‘yan Najeriya su jira matsayin da shugaba Muhammadu Buhari zai dauka inda ya yi kira da a duba halin ha’ula’i da ‘yan kasa ke ciki don saukake musu wahalhalu da suka sha.

Ko yaya ‘yan kasa ke ganin wannan al’amari, Malam Ibrahim mai kantin sayar da kayayyakin amfani na yau da kullum ya ce suna cikin mawuyacin hali.

Duk kokarin ji ta bakin babban bankin Najeriya a game da matsayar da ya dauka a game da tsoffin takardun kudin a yayin hada wannan rahoto dai ya ci tura.

Idan Ana iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnonin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar da kara a babban kotun don neman a tsawaita wa’adin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi don rage wahalar da yan kasa ke ciki inda daga bisani, kasa da sa’o’i 72, kotu ta dakatar da bankin CBN daga aiwatar da wa’adin ranar 10 ga wata na daina amfani da tsoffin takardun na 200, 500 da ma dubu 1.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
XS
SM
MD
LG