Duk da barazar bakawa gonakin wasu manoma wuta da 'yan-bindiga su ka yi a wasu yankunan Birnin Gwari makonni biyu da su ka gabata, sulhun da gwamnatin jahar Kaduna ta assasa ya fara aiki.
Shirin Manuniya na wannan mako ya maida hankali ne akan maganar shugabanci da tsaro a Najeriya sai kuma shirye-shiryen Zaben shugaban kasar Amurka.
Daya daga cikin 'yan uwan wadanda suka rasu ya ce kokarin kaucewa mai babur a kan kwana ne ya sa babbar motar ta afkawa motar da ke dauke da masu Mauludin
A cigaba da nuna bacin rai da kungiyoyi da daidaikun 'yan Najeriya ke yi kan al'amura masu nasaba da rashin tsaro, likitoci matasa sun ja kunnen hukumomi.
Jami'an tsaro a Najeriya sun sanar da samun nasarar kashe wani kasurgumin dan bindiga mai suna Alhaji Kachalla Ragas, wanda ya shahara wajen kai hare hare da kuma satar mutane domin neman kudin fansa a wasu sassan jihar Kaduna da jihohi makwabta.
A kokarin kawar da 'yan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta sanar da cewa rundunar sojan Najeriya ta hallaka kasurgumin 'dan bindigar nan mai suna Buhari Alhaji Halidu. Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da aikin kai hari kan 'yan bindigar a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Domin Kari