Garin na Ma’undu dai dake yankin karamar hukumar Mariga a yanzu kusan kashi takwas daga cikin goma na mutanen garin sun tsere suna gudun hijira saboda tashin hankalin ‘yan bindiga.
A cikin jawabin Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce ya ga abin takaici ganin babban gari irin wannan amma babu kowa.
“Allah ya kawo ni kuma na ga garin Ma’undu, abin takaici ne a ce babban gari kamar wannan amma babu mutum ko kwaya, duk sun yi gudu hijira, amma da yardar Allah muna sa ran nan da dan lokaci kadan kowa zai dawo gidajensu”
Su ma dai wasu daga cikin Mutanen garin sunyi farin ciki da zuwan Gwamnan tare da fatar daukar matakin da zai sa su koma gidajensu.
Jami’an tsaron dai sun ce sun kara jan damara akan yaki da miyagun a karkashin wani shiri na musamman na yaki da ‘yan bindigar da suka addabi jihohin dake fama da ta’addanci a cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Monday Bala Kuryas wanda ke cikin tawagar Gwamnan.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: