Majalisar ta maida hankalinta kan kasar inda tayi nazari akan irin halin da kasar ke ciki musamman dangane da yajin aikin da wasu kungiyoyin kwadago suka fantsama ciki duk da umurnin da kotun dokokin ma'aikata ta bada cewa kada su shiga yajin aiki.
.Ministan watsa labarai na kasar Alhaji Lai Muhammad yace majalisar ta gamsu 'yan Najeriya sun fahimceta kuma an gano cewar duk matakan da ake dauka na kawo gyara ne. Ya kuma jinjinawa wani bangaren kungiyar 'yan kwadago da bai yadda ya shiga yajin aikin ba tun ma kafin kotun ta haramba yin shi.
Kodayake gwamnati ta ce zata dauki matakan kawo sulhu da masalaha ministan shari'a na kasar Abubakar Malami yayi tsokaci akan bijirewa umurnin kotu da wani bangaren kungiyar kwadago ya yi. Yace dole ne doka tayi aiki a kowane lokaci a cikin kasa. Yace lamura ne da suka jibanci da'a da doka da oda. Yace duk abun da mutum zai yi a kasa doka tayi tanadi a kai. Yace kodayake ba za'a hana mutum ya yi yadda yake so ba amma kuma dole ne ya fuskanci doka idan ya ki da'a da bin doka da oda.
Matsayin gwamnati yanzu shi ne akan da'a da bin doka kuma duk wani yunkuri na kin bin doka ba za'a kawar da kai ba. Za'a tabbatar ainihin doka tayi aikinta.
Ga karin bayani.