NIAMEY, NIGER -Makwanni biyu a Nijar bayan hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum, Majalissar soja ta CNSP ta bayyana sunayen Ministocin sabuwar Gwamnatin rikon kwaryar kasar a yayinda Shugabanin kasashen Yammacin Afrika ke taro a wannan Alhamis a Abuja don nazarin hanyoyin da za su bullo wa rikicin siyasar ta kasar.
Sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya wacce Firai Minista, kuma Ministan kudin kasa Ali Mahaman Lamine Zeine zai jagoranta na da mambobin 21 da suka hada da fararen hula galibi bakin fuskoki da mata hudu da wasu daga cikin hafsoshin sojan da suka yi juyin mulkin na 26 ga watan Yuli.
Shugaban kungiyar Voix des Sans Voix Nassirou ya bayyana gamsuwa da tsarin da Majalissar ta CNSP ta yi amfani da shi wajen wadannan nade-nade.
‘Dan rajin kare dimokrdaiya Abdou Elhadji Idi na hadin guiwar kungiyoyin FSCN shi ma ya yaba da yadda aka takaita yawan Ministocin Gwamnatin ya gano wasu kurakuren da ka iya shafar sabuwar tafiyar da aka sa gaba.
Sabuwar gwamnatin na da mata hudu wato kashi 1 daga cikin 5 na yawan mukamai, to amma a cewar jigo a Kungiyar M62 Falmata Taya girman tangardar da suka hango ta fice batun kason jinsin mata.
Wannan na wakana a yayin da shugabanin kasashen Yammacin Afrika mambobin ECOWAS ke gudanar da taro an Abuja a wannan zama na neman mafitar dambarwar siyasar kasar da a yanzu haka ke fama da hare-haren ta’addanci. Na baya-bayan nan shine wanda ya yi sandiyar mutuwar jami’an tsaro guda biyar a jiya Laraba a kauyen Bourkou Bourkou na Jihar Tilabery.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna