Ana dakon matsayar da kungiyar ECOWAS za ta cimma a taron da take yi a Abuja, babban birnin Najeriya a wani yunkuri na shawo kan rikicin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
Mambobin kungiyar mai dauke da kasashe 15, sun ce za su bi hanyar diflomasiyya wajen kawo karshen rikicin, amma har yanzu batun amfani da karfin soji na daga cikin zabin da za su iya amincewa - wanda suka ce zai zamanto zabi na karshe.
A ranar Lahadin da ta gabata, wa’adin mako guda da kungiyar ta ba sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya cika.
Kungiyar ta nemi jagororin juyin mulki da su mayar da kasar kan turbar dimokradiyya su kuma saki Shugaba Muhamed Bazoum ko kuma su dauki matakin soji a kan su.
Sojojin sun yi kememe sun yi biris da barazanar, sun kuma ci gaba da kafar gwamnatin wucin gadi a kasar.
Tun bayan aukuwar juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, kungiyar ta ECOWAS ta sakawa kasar takunkumai, ciki har da wadanda ta saka a farkon makon nan.
Taron na ECOWAS na gudana ne yayin da rahotonni a ranar Laraba ke nuni da cewa abincin da Bazoum ke ci ya kusa karewa kuma yana zaune ne a wani irin mummunan yanayi.
Masu fashin baki na nuni da cewa kungiyar ta ECOWAS ta shiga tsaka mai wuya duba da cewa jama'a da dama na adawa da daukan matakin soji.
Kazalika, sojojin da suka yi juyin mulkin na ta bijirewa duk wani yunkuri ko tawaga da aka tura don shiga tsakani.
A ranar Laraba, Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi ya kai ziyara Nijar inda ya gana da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tchiani.
Sanusi ya fadawa manema labarai cewa ziyarar da ya kai Nijar ta gashin kansa ce, ba shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ba ne ya tura shi.
Tinubu shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS.
Jim kadan bayan dawowarsa, Sanusi ya y wata ganawar sirri da Tinubu.
Juyin mulkin na Nijar shi ne na hudu da ya faru cikin shekaru uku da suka gabata a yankin yammacin Afirka.
Mali, Burkina Faso da Guinea duka suna karkashin mulkin soji bayan juyin mulki da aka yi a kasashen.
Dandalin Mu Tattauna