Kudurin ayyana dokar ta baci da Sanata mai wakiltar jihar Neja ta gabas, Sani Musa ya gabatar wa Majalisar ya samu karbuwa. Amma wasu ‘yan Majalisar na ganin a fara daukar matakin sulhu da ‘yan ta’addar domin kubutar da daliban kafin saka dokar ta bacin.
Satar ‘yan makaranta na neman zama ruwan dare a Arewacin Najeriya, idan aka yi la’akari da wadanda suka faru a baya, da suka hada ‘yan makarantar Chibok a jihar Borno da ‘yan matan Dapchi a jihar Yobe, sai kuma ‘yan makarantar Kankara a jihar Katsina; ga kuma wannan da ya faru a makarantar Kagara ta jihar Neja.
Ganin yadda wannan matsala ke neman rikirkitar da harkar ilimi a makarantun jihohin arewacin Najeriya, wasu Sanatoci na ganin ya zama dole a samar da matakan tsaro don kare makarantu baki daya.
Da yake magana da sashen Hausa na Muryar Amurka, Sanata mai wakiltar jihar Kebbi ta Kudu Bala Ibn Na Allah, ya ce dukkanin sace-sacen dalibai da ake yana faruwa ne a yankin Arewa kadai, kuma ya Kamata gwamnati ta yi tunanin daukar matakin gaggawa don magance matsalar.
Amma shi kuma Sanata mai wakiltar Zamfara, Hassan Nasiha Jarman Gusau, na ganin daukar matakin sulhu da ‘yan bindigar kamar yadda aka taba yi a yankin Niger Delta, kuma ake yi a yankin Zamfara shi ne mafita.
Kwararre a fannin kimiyyar tsaro na kasa da kasa, Dakta Kabir Adamu, na ganin wannan mataki da Majalisa ta dauka shi ne daidai, domin tabbatar da tsaron al’umma shi ne babban aikin Majalisar Zartarwa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, jihar Borno, jihar Neja, Abubakar Sani Bello, Nigeria, da Najeriya.