Masu ruwa da tsakin dai sun yi kira da kakkausar murya ga ‘yan Najeriya musamman matasa da su gujewa fadawa cikin tarkon ramuwar gayya suna masu cewa, hakan ka iya jefa kasa cikin rudani.
Fitaccen lauya, Barista Mainasara Kogo Ibrahim, ya ce kamata ya yi gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su fito a yi maganin lamarin kada ya yi nisa.
Shima malamin addinin Islama, Suleiman Nasir Ahmad, ya bukaci ‘yan kasa su yi hakuri.
A bangaren iyaye mata, Malama Bilkisu Kaikai, ta bai wa al’umman arewacin Najeriya na ta shawaran kan lamarin.
Shaidun gani da ido dai sun ce rikicin ya barke ne bayan rashin fahimta da ya ufku tsakani wani dan dako da wata mai shago a kasuwar Sasa dake birnin badun lamarin da rikide zuwa rikici da ya yi sanadiya rasa rayuka da dukiyoyi.
Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari na musamman kan sha’anin yadda labarai, Malam Garba Shehu, a shafinsa na tuwita ya ruwaito cewa, gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta zata yi duk mai yiyuwa wajen tsaron rayuka da da dukiyoyin duk yan kasa gabaki daya:
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf a Sauti: