Da misalign karfe uku na daren talata, wayewar laraba ne ya kamata ayarin farko na maniyyatan Nijer ya tashi zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali, to amma sai bayan da maniyyatan suka taru sa’an nan aka bayyana masu cewar an dage tafiyar a dalilin rashin isowar jirgi.
Daraktan kamfanin jigilar alhazan Alhaji Abdul’azizi Idrisa ya bayyanawa wakilin muryar amurka a yamai Sule Mumuni Barma, cewar sun bukaci kowanne maniyyaci ya koma gida har sai an waiwaye shi.
Wata majiya ta bayyana cewa akwai wani tsohon bashi tsakanin hukumomin kasar ta Nijer da kamfanin da aka ba kwangilar jigilar alhazan bana, ta dalilin haka ne ya yanke shawarar sai an biya shi sa’an nan ya soma wannan aiki.
Sai dai hukumar alhazan ta bakin maga takardan ta Malam Nuhu Sallau ta ce ba haka batun yake ba, wasu ‘yan matsaloline suka hana jirgin zuwa kuma za’a shawo kan lamarin bada dadewa ba.
Ya ce baza su iya sanin cewar kamfani bashi da jirgi a hannu ba, domin hukumar alhazan ta taba aiki dasu shekaru da dama.
Domin Karin baya ni, ga rahoton Sule Mumuni Barma.