Bayan alhazan sun hallara suna gap da shiga mota da zata kaisu filin jirgin sama sai aka sanar dasu cewa jirgin bai zo ba saboda haka kowa sai ya koma gidansa sai an waiwayeshi.
Daraktan kamfanin sufurin Abdulaziz Idrisa yace shi bai san abun da ya faru ba. Su dai an fada masu jirgin bai iso ba sai nan da kwanaki biyu.
Sai dai wata majiya tace akwai tsohon bashi tsakanin kamfanin da gwamnatin Nijar wanda sai an biya kamfanin zai soma jigilar maniyattan. Amma hukumar alhazai ta musanta wannan magana. Yace su basu san da miskilar da kamfanin ya samu ba.
Maniyatta kimanin dubu goma sha biyu da dari bakwai da sha biyu ne zasu tafi aikin hajjin bana daga Nijar. Inji hukumar alhazan Nijar, komin dadewa ranar daya ga watan gobe ne za'a kammala jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.