Shaidun da kamfanin dillacin labarai ya yi hira da su, sun ce sojojin sun yiwa wani dan jarida kissan gilla, a gaban idon‘yan kasashen ketaren, da nufin razana su.
Kamfanin dillancin labaran ya kuma ce, mutanen dake otel din da ‘yan kasashen ketare da kuma‘yan kasar Sudan masu hali suka fi zama, sun dauki sa’oi suna neman taimako daga dakarun wanzar da zaman lafiya, wadanda nisan inda suke bai mai tazarar kilomita daya ba, da kuma ofishin jakadancin Amurka.
Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Powers ta bayyana gazawar gwamnatin Sudan ta Kudu, da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Tace a cikin shekaru uku da suka shige, gwamnatin Sudan ta Kudu tana kauda kai ana aikata kisan kai da fyade.
Da aka tambayeshi dalilin da yasa MDD tayi watsi da neman dauki da aka yi, sai kakakin babban magatakardar Farhan Haq yace, MDD tana daukar wannan rahoton da muhimmanci kuma zata yi cikakken bincike.
Powers ta kuma yi tsokaci a kan zargin da shaidu suka yi a hirarsu da kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, ofishin jakadancin Amurka ya yi watsi da kiran da aka yi na neman taimako. Tace ofishin ya dauki mataki nan da nan ya kuma tuntubi jami’an gwamnatin kasar Sudan da Kudu, wadanda suka tura dakaru domin shawo kan lamarin.
An kai harin ne yayin wani gumurzu na kwana uku a Juba tsakanin dakarun shugaba Salca Kiirr na SPLA da na wadanda ke goyon bayan mataimakinsa Reik Machar. Fadan ya yi sanadin kashe a kalla mutane dari biyu da saba’in, ya kuma sa kimanin mutane dubu talatin da shida kauracewa matsugunancu, abinda ya kuma jefa yarjejeniyar da aka cimma a watan Agusta shekara ta dubu biyu da goma sha biyar cikin halin kila-wakala.