Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Sakamakon Zabe Ana Zaman Zullumi da Dar Dar A Zambia


Shugaba Edgar Lungu da aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben
Shugaba Edgar Lungu da aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben

Ana zaman zullumi da dar dar a Zambia, kasar da take tinkaho wajen gudanar da zabenta cikin lumana.

Bayan da shugaban kasar ya lashe zaben da 'yar karamar rata a makon jiya, 'yan hamayya suna zargin an yi magudi a zaben kuma suna shirin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.

Shugaba Edgar Lungu yace zai jinkirta bikin ranstuwarsake kama aiki dake shirin sai makon gobe, yayinda kotun tsarin mulkin kasar take duba zarginda 'yan hamayyar suke yi. Kotun tana da mako biyu kamin ta yanke hukunci.

Jiya talata rundunar 'Yansandan kasarta bada labarin ta damke magoya bayan 'yan hamayya a fadin kasar wadanda take zargin suna lalata kadarori jam'iyyar da take mulkin kasar.

Runduanar tace mutanen sun cunnawa motoci wuta suka yi garkuwa da 12 magoya bayan jam'iyyar da take mulkin kasar. Wasu daga cikinsu an kamasu ne kan zargin tada rigima da dai wasu dalilai, kamar yadda kakakin shugaban kasar ya gayawa shirin Muryar Amurka na turanci.

Haka nan yace ana tsammanin jami'an tsaro zasu iya kama karin wasu mutane a wani lardin kasar dake kudanci, inda nan ne babbar jam'iyyar 'yan hamayya take da karfi.

XS
SM
MD
LG