Kasancewar akwai wadandasu da suka rasu, akwai kuma wadanda yanzu shekarun sun kai su jefa kuri'a saboda haka wajibi ne a sabunta sunayen al'umma.
Hukumar ta soma aikin sabuntawar ne tun biyu ga watan Janairu na wannan shekarar kuma an bata har zuwa talatin da daya na wannan watan da muke ciki saboda yana cikin dokokin hukumaar da aka gindaya mata.
Sakataren hukumar ya yi bayani akan yadda mutane su ke fitowa domin sabunta sunayensu. Yace sun samu nasara kuma makonni ukku ke nan da suke ta kokarin lissafa sunayen da suka samu.
Kasar zata yi zaben shugaban kasa a shekarar dubu biyu da goma sha takwas dalili ke nan da hukumar ke kokarin gyara kura-kuranta.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.