Rashin komawar yayan jam’iyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya zuwa PDP ya kara nuna alamun cewar jam’iyar PDP bata da karbuwa a yankin kudu maso yanmacin najeriya, yankin da kabilar yarbawa sukafi yawa, wayanda kuma ake ganin suna goyon bayan jam’iyar APC sama da kasa.
Daga cikin yan jam’iyar APC da suka sauya sheka akasarin su sun koma jam’iyar ADC ne, wata sabuwar jam’iya mai alaka da tsohon shugaban kasa Dr Olusegun Obasanjo, wanda kuma ya kudiri aniyar ganin kawo karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shekara mai zuwa na 2019.
Daya daga cikin yan majalisar daga jihar Oyo sanata Adesoji Akanbi da a jiya aka ce ya koma ADC ya musanta wannan labarai, inda yace shi yana nan daram dakam cikin APC.
Wasu mutane da dama na cewa dalilin da ya sa yan jam'iyar APC ke sauya jam'iya zuwa PDP , saboda basa son gyara ne, yayinda wasu da dama ke dora laifin akan gwamnatin Muhammadu Buhari wanda haka ka iya janyo ci baya ga jam'iyyar APC mai mulki.
Wannan lamarin ya sanya mutane nazarin cewa ko yan majalisun da suka sauya sheka zasu iya cin zabe ba tare da Buhari ya daga hannun su ba, shine abin a jira a gani.
saurari rahoton Babangida Jibril
Facebook Forum