Wani babban jami’in yan sanda ya fadawa Muryar Amurka dan kunar bakin waken ya kaiwa wani taron jama’a da suke rumfar zabe a Quetta hari ne a kan babur.
Wadanda harin ya shafa sun hada ne da masu kada kuri’a da yan sanda da wakilan yan siyasa.
Akber Khan ya kada kuri’arsa a rumfar zaben kuma ya shedi lamarin.
Yace na kada kuri’a ta a rumfar zaben. Ina jin gajiya a jikina sai na koma shago na samu abin sha mai sanyi, bayan haka ina fita a gaban shago sai na kasa tafiya yayin da wannan fashewar ta tashi.
Kungiyar IS mai tsaurin ra’ayin Islama ta dauki alhakin kai harin na yau laraba a garin Quetta, babban birnin gundumar Baluchistan, inda aka taba kashe mutane 149 a wurin wani gangamin taron siyasa a watan da ya gabata
Zaben nay au Laraba shine na cikon uku kacal da Pakistan zata canza gwamnati cikin zaman lafiya.
Facebook Forum