Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Yi Wa Masu Yoyon Fitsari 150 Aiki Kyauta a Borno


A man pours fake fuel on the face of a protester as they perform at a demonstration against the fossil fuel industry during the U.N. Climate Change Conference (COP26), in Glasgow, Scotland.
A man pours fake fuel on the face of a protester as they perform at a demonstration against the fossil fuel industry during the U.N. Climate Change Conference (COP26), in Glasgow, Scotland.

Hukumar lura da yawan jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ta ce akwai mata kusan dubu 150 da ke fama da lalurar yoyon fitsari a Najeriya.

Wakilin hukumar Majalisar Dinkin Duniya Dakta Eugene Kongnyuy, ya bayyana hakan ne a yayin da hukumar ke yi wa wasu mata masu lalurar ta yoyon fitsari aiki a garin Maiduguri.

Ya ce a kasashen da suka ci gaba, ba a samun wannan lalurar don tuni aka kawar da ita, amma a Najeriya ta yi tsamari inda mata kusan dubu 150 ke fama da ita. Wannan ya jefa mata da dama a cikin rayuwar kunci a yayin da akasarinsu ke fuskantar tsangwama

Yoyon fitsari babbar matsala ce a Najeriya musamman a jihar Borno, a cewar wakilin. Kodayake babu wani takamaiman alkalumma a jihar da za a iya dogara da su, amma saboda ana samun yawan mace-mace a wajen haihuwa kuma inda akwai hakan to dole ne a samu matsalar yoyon fitsari.

Masana sun ce yawanci lalurar na faruwa ne sakamakon auren wuri inda kugun mace bai yi kwari ba ko kuma nakuda mai tsawon lokaci.

Wata mai fama da lalurar ta ce kamu ne bayan haihuwarta ta farko inda ta kwashe kwanaki uku a asibiti ta na nakuda daga bisani likitoci suka yi kokari ciro yaron da karfi, amma wajen jawo shi aka ji mata rauni.

Saurari rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG