Sanin kowa ne zazabin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan dake haddasa asarar rayukan kanannan yara. Yanzu haka ma'aikatan asibiti ne a Jamhuriyar ta Nijar ke bin gida-gida suna rarraba maganin.
Maganin da ake kira CPS a takaice, wanda a cewar wata jami'ar kiwon lafiya Hajiya Yaha a asibitin PMI Stade dake Damagaram, ta ce bada maganin yayi tasiri a yadda suka lura, yanzu babu yawaitar cutar tunda aka fara amfani da maganin, su ma iyaye sun himmatu wajen kai yaransu asibiti don karbar maganin.
Hajiya Yahar ta kuma bayana irin sauyin adadin mutanen da ke shigowa da zazzabin cizon sauro inda ta ce yanzu a sati sukan samu mutane 20 zuwa 25 sabanin a da da ake samun har mutane akalla 700 dauke da zazzabin cizon sauro a cikin sati daya kawai. Ga cikakken rahoton cikin sauti daga kasa.
Facebook Forum