Congo ta ce ta kawo karshen matsalar barkewar cutar Ebola a kasar, inda ta ce hanzarin da jami’an kiwon lafiya da hukumar lafiya ta Duniya WHO suka nuna, shi ya taimaka wajen dakile cutar.
Jiya Talata, ita ce rana ta 42 da ba a samu sabon mutum da ya kamu da cutar ba.
Ka'idar shawo kan cutar ta Ebola, sai an kwashe kwanaki 21 sau biyu domin shi ne wa'adin da cutar ke bayyana a fili ko ta yi kyankyasa.
“Gwamnati ta yi kokari wajen daukan matakai da kuma neman tallafi cikin hanzari tare da wayar da kan jama’a kan barkewar cutar da hadurran da ke tattare da ita.,” inji shugaban WHO, Cif Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Ya kara da cewa “irin wannan shugabanci shi ya kubutar da rayuka.”
Wani mai magana da yawun hukumar ta WHO, ya dora nasarar da aka samu akan wani “sabon bincike na alluran rigakafin cutar” wanda ya ce ya ba da kariya ga mutum 3,000.
Sai dai duk da haka, cutar ta halaka mutum 33 a wannan karo.
Facebook Forum