Kimanin wata guda ke nan tunda hukumar 'yansandan Uganda suka yiwa madugun 'yan adawa Kizza Besigye daurin talala bayan zaben shugaban kasa na ranar 18 ga watan Fabrairu.
Tun daga lokacin jami'an 'yansandan kasar sun kama dan adawan sau tara , wato duk lokacin da ya yi yunkurin fitowa daga gidansa.
Amurka da Tarayyar Turai sun sha kiran mahukuntan Uganda da su sako dan adawan ba tare da bata wani lokaci ba. To saidai mai magana da yawun 'yansandan kasar Fred Enanga yace suna tsare da Besigye ne bisa doka.
Fred Enanga yace "kuna sane da dalilan da suka sa rundunar 'yansanda ta dauki matakan hana barkewar tashin hankali a karkashin doka mai lamba 24 ta 'yansanda. Dokar ta ba 'yansanda ikon daukan matakan da zasu hana aukuwar tashin hankali da suka hada da daurin talala idan rundunar tana ta tabbaci cewa barin wani ko wasu suna yawo suna saduwa da wasu zai jawowa jama'a illa ko kuma ya shafi zirga zirgan ababen hawa"
Banda hana Besigye fita 'yansandan sun kuma hana mutane su ziyarci Besigye a gidansa ko kuma su gana dashi. Ko iyalansa ma an takaita saduwarsu dashi. Bugu da kari an hana motoci shiga gidansa