An sake kama madugun 'yan adawa Kizza Besigye na kasar Uganda karo na biyu yau Juma'a bayan da sakamakon zaben da suka fara fitowa na nuna cewa shi ne ya zo na biyu.
Shaidun gani da ido sun ce 'yansanda sun yi awan gaba da Mr. Besigye tare da wasu kusoshin jam'iyyarsa wato Forum for Democratic Change daga hedkwarsu dake birnin Kampala.
Kafin su kamashi sai da 'yansandan suka harba barkonon tsohuwa cikin ginin hedkwatar jam'iyyar yayinda shugabannin jam'iyyar ke shirin gudanar da taro da manema labarai inda suka yi aniyar gudanar da irin magudin da aka tafka a zaben..
Wani dan takarar neman kujerar shugaban kasa tsohon firayim ministan kasar Amama Mbabaziya bar gidansa yau Juma'a tare da 'yansanda. Tun farko Mbabazi ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa 'yansanda suna kame kamen mutane kusa da gidansa. Ya kuma fitar da bidiyon da ya nuna 'yansanda suna sintiri a titunan dake unguwarsa.
Sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta fara fitarwa yau Juma'a sun nuna Shugaba Yoweri Museveni na kan gaba da kashi 62 cikin dari na kuri'un da aka kirga yayinda Besigye yake da kashi 32. Mbabazi dake binsu a baya ya samu kasa da kashi biyu.