Ministan Kudin ajeriya tace da masu saka jari daga ketare suna zuwa ne da korafi amma yanzu lamarin ya canza.
Yanzu 'yan kasuwan na maganar shiga hada hadar kudi ne da Najeriya. Sai dai Yushau Aliyu wani masanin tattalin arziki yace hakan zai yi nasara ne kawai idan aka sauya matakin rufe iyakokin kasar.
Yusuf Aliyu yace dole ne gwamnati ta sake duba kasuwancin da ya shafi iyakoki saboda kasuwancin kasa da kasa da bankuna ke taimakawa 'yan kasuwa suna samun riba. Ribar da suke ci zata taimakawa 'yan kasuwan da ma gwamnati.
Wani masanin tattalin arziki da harkokin noma Dr. Sani Yakubu Gombe na ganin kai tsaye za'a cimma muradun. Yace ya zagaya gonaki a wurare daban daban ya gano cewa nan da dan lokaci kadan za'a wadatu da abinci iri iri.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.