Ministan yayi misali da wurin da ya fito, Birnin Magaji, inda yace mazauna wasu kauyukan suna hada baki wurin kunkuma sata musamman satar shanu, hatta a kauyensa an samu irin wadannan mutanen.
Yace sai da gwamnatin Buhari ta zo aka yi hobasan shawo kan lamarin. Yace sun yi atisahi a duk dazuzukan kamar a jihar Zamfara da zummar fatattakan barayin.
Yace idan sojojinsu zasu je wurin sai su yi masu waya suna zuwa. Kwanakwanan nan suka je kauyen Dumburum dake cikin karamar hukumar Zurmi inda suka samu shanun da aka sace wajen dubu ukku amma mutanen sun gudu.
Yanzu gwamnati na shirin kara sojoji a jihar Zamfara domin bataliya guda bai isa ba.
Dangane da yaki da Boko Haram yace suna iyakar kokarinsu. Duk abun da Boko Haram ke cewa yanzu farfaganda ce kawai. A kan sojoji kuma yace duk abun da suke bukata ana basu daidai gwargwado.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.