Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Da Masana’antun Da Zata Iya Sarrafa Kayayyaki Masu Inganci


Kamfanin sarrafa iskar gas na Najeriya
Kamfanin sarrafa iskar gas na Najeriya

Masana a harkar masana’antu sun bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki almundahana da makarkashiya da wasu jami’an gwamnati ke yi wajen durkusar da masana’antun Najeriya da sunan zawarcin masu saka jari daga kasashen ketare.

A wani taron manema labarai karkashin shugabancin tsohon mataimakin shugaban kwamitin kudi na Majalisar Wakilai Leo Dilkon, yace Najeriya tana da masana’antu da kayayyakin da zata sarrafa dake da inganci fiye da wadanda ake shigowa da su daga kasashen waje, amma wasu jami’an gwamnati suna kawo cikas ga kokarin gwamnatin tarayya na farfado da shiri dogaro da kai.

Leo Dilkon wanda shine ya mallaki kamfanin Hamtul Press, dake da injinan buga takardu da yin jakankuna da kyankyasar kaji da sauran amfanin gona, yace matakan da wasu jami’an gwamnati ke gindayawa suke hana ci gaban masana’antu a Najeriya.

Wasu masu aiki a masana’antu da suka halarci wannan taron sun bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji, cewa rashin kayayyakin aiki ya hana su gudanar da aikinsu wanda a cewarsu ya janyowa dinbin matasa gararanba a titunan Najeriya.

Saurari cikakken rahotan Zainab Babaji daga Jos.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

XS
SM
MD
LG