Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikin Da Ta Ke Da Wata Biyu


Kungiyar ASUU
Kungiyar ASUU

Kungiyar malamaman jami’o’in Najeriya wato ASUU ta bayyana cewa ta tsawaita yajin aikin gargadi da ta fara a watan jiya, wanda ta fara wata daya tak da ya gabata.

Kungiyar dai ta sanar da wannan matsayin na ta ne bayan taron kolinta da ta gudanar a ofishinta da ke cikin jami’ar birnin tarayya Abuja wanda ta fara daga ranar Lahadi zuwa safiyar yau Litinin.

ASUU dai ta tabbatar da cewa ta kara tsawon yajin aikin da take yi ne wanda ta fara wata daya da ya cika cak a yau 14 ga watan Maris na shekarar 2022 daga wata daya zuwa wata uku don ba wa gwamnatin Najeriya isasshen lokacin sanin mutuncin bangaren ilimin jami’o’i a kasar.

Kungiyar ta kara da cewa manyan abubuwa guda biyu suka yi sanadin shigarta yajin aikin gargadi da take ciki kuma sun hada da hanyar da gwamnati ke biyan malamanta wato tsarin biyan albashi na IPPIS wanda ke cike da rashin daidaito inda su kuma malaman ke ganin bai dace da tsarin yadda suke aiki ba, suka samar da nasu tsarin da manhajar biyan albashi a bayyane da bin diddigi na jami’o’i, wato University Transparency and Accountability Solution, (UTAS) a turance.

Haka kuma, kungiyar ASUU ta bayyana rashin jin dadinta a game da ikirarin babban daraktan hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Kashifu Inuwa, wanda ya ce manhajar da kungiyar ASUU ta samar na UTAS ta kasa tsallake gwajin inganci guda uku da suka hada da na yarda da mai amfani, da rauni da kuma damuwar masu amfani wanda hukumar NITDA ta gudanar kan manhajar.

Dakta Kashifu ya kara da cewa hukumar NITDA bayan gwaje-gwajen da ta ta yi kan manhajar guda uku ta tattara rahoto kuma ta mika wa ma’aikatar da NITDA ke karkashinta da sauran masu ruwa da tsaki da hakkin ganin wannan rahoto da kuma aiwatar da shi har da kungiyar ASUU akan abin da gwajin ya gano kan manhajar UTAS da suka gabatar.

NITDA dai ta kara da cewa a halin yanzu dai kungiyar ASUU na aiki kan rahoton da ta mika mata don ganin ta gyara matsalolin da ta gano manhajar ke da su.

A bangaren kungiyar ASUU kuwa ta dage cewa gwajin da NITDA ta yi wa manhajar UTAS ya sami cika gwajin inganci a bisa kaso 85 da kuma 77 cikin 100, ta na mai cewa idan aka yi amfani da adalci hakan ya cika awon inganci na komai.

ASUU ta kuma yi barazanar sakin rahoton da hukumar NITDA ta bata na shaidar cewa manhajar UTAS ta samu kaso 85 na gwajin da ake kira da User Acceptance Test wato UAT matukar hukumar ta ci gaba da yin ikirarin manhajar ba ta tsallake gwajin da ta yi mata ba.

Idan ana iya tunawa wasu daga cikin muhimman dalilan da ya sanya ASUU tsunduma cikin yajin aikin gargadin da ta fara tsawon wata daya da ya gabata su ne tsarin biyan albashin mambobinta na IPPIS da kuma rashin cika alkawarin biyan basussuka da gyarar albashi na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ASUU da gwamanatin Nigeria kan albashi a shekarun baya.

Kungiyar dai ta ce yin amfani da manhajar UTAS da ta kirkiro zai bata damar cin gashin kanta gurin kula da aikinta ba ta IPPIS da gwamnati ta kakaba mata ba.

Baya ga wannan muhimman bukatun kuwa, akwai wasu kananan da duk sun ta’allaka ne wajen samar da ingantaccen ilimi da wajen karatu ga malamai da daliban jami’o’in gwamnatin tarayyar kasar da ma gwamnatocin jahohi da kuma hanyar karin matsayi ga malaman.

XS
SM
MD
LG