Barazanar fadadar yakin a kan iyakar Isra'ila daga arewa na daga cikin bayanan da aka tattauna akai a jiya Alhamis a Washington, inda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da mai bada shawara kan harkokin tsaron kasa a fadar White House Jake Sullivan suka gana da mai bada shawara kan harkokin tsaro na Isra’ila Tzachi Hanegbi, da Ministan kula da tsare tsare Ron Dermer.
Tattaunawar tasu ta kuma tabo batutuwa kan kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, da tabbatar da sako dukkan sauran mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, da kuma kara kai agaji ga Falasdinawa farar hula.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya fada wa manema labarai yayin wani taro a Isra'ila da Hezbollah, kawancen Hamas cewa, "Mun damu matuka game da halin da ake ciki a arewacin Isra'ila. Mun ga kungiyar Hezboallah tana kara kai hare hare kan kauyukan Isra'ila da wuraren jin dadin fararen hula, sabili da haka mu ke daukar matan diflomasiya na ganin lamarin bai ta'azzara ba."
Bangarorin biyu sun yi musayar wuta tun a watan Oktoba, lokacin da yakin Gaza ya barke.
A cikin watanni 8, an kashe fiye da mutane 400 a Lebanon, akasarinsu mayakan Hizbullah, amma kuma akalla fararen hula 80. A Isra'ila, an kashe sojoji 16 da fararen hula 11 a fadan.jiya Alhamis.
Dandalin Mu Tattauna