Masu zanga zanga sun fara maci ne a wajajen karshen watan jiya kan shirin gwamnati na fadada babban birnin kasar Addis Ababa. Masu sukar lamirin shirin a yankin kabilar Oromo sun ce shirin zai raba kananan manoma da muhallansu, da kuma 'yancin da suke da shi.
Amma gwamnatin kasar ta ce, adadin wadanda suka mutu sakamakon zanga zangar mutum biyar ne, banda 'Yansanda hudu wadanda tace an kashe su ranar Talata a yankin Oromo.
Ahalinda ake ciki kuma, Amurka tayi kira ga mahukuntan Najeriya su binciki arangamar da aka yi tsakanin 'yan shi'a da dakarun kasar, lamari da rahotanni suka ce ya halaka daruruwan mutane.
Ofishin jakadancin Amurkan dake Abujan Najeriya, jiya Laraba, yace tilas ne gwamnatin cikin hanzari, kuma a bayyane, ta gudanar da bincike kan wannan lamari, kuma ta hukunta duk wadanda aka samu suna da hanu a ciki.