Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya na Cigaba da Samun Nasara Akan 'Yan Boko Haram


Sojojin Najeriya na cigaba da farautar mayakan sa kan boko haram a dajin Sambisa da sauran wurare, tare da ceto wasu da 'yan kungiyar suka yi garkuwa da su.

Kimanin ‘yan boko 49 ne rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe a cikin ‘yan kwanakin nan sannan ita kuma rundunar sojan ta rasa jami’an sojanta biyu, daya daga cikinsu na da mukamin laftanan kanal sakamakon yakin da suke cigaba da yi da maharan a arewa maso gabashin Najeriya.

Majo-Janar Yushe’u Abubakar, shine babban kwamandan da ke kula da wannan shiyar ta arewa maso gabashin Najeriya, dake shiya ta 7 a garin Maiduguri, ya shaidawa manema labarai cewa suna samun nasara wajen yakin da suke yi da ‘yan boko haram.

Ya kuma ce yanzu haka sun sami kutsawa cikin dajin Sambisa inda suka kwato kayayyakin yaki da dama daga hannun maharan, suka kuma kubutar da wasu mutane kusan su 154 , wanda cikinsu har da dattijai da suka kai kimanin 85, da mata da yara wadanda maharan suka yi garkuwa da su.

Majo-Janar Yushe’u ya kara da yin kira ga jama’a da su cigaba da basu hadin kai ta hanyar basu bayanan duk wani da suke kyautata zaton da boko haram ne ko sun ga alamar ana kitsa wani abu da bai dace ba, ta haka ne za su iya daukar mataki.

Ga karin Bayani daga Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG