Gwamnatin jamhuriyar Niger ta bada sanarwar cewa a ranar ashirin da daya ga watan Disamban shekara ta dubu biyu da goma sha biyar idan Allah ya kaimu za'a fara yakin neman zabe a kasar.
Ministan shari'a na kasar, wanda kuma shine mai magana da yawun gwamnati, Moro Amadou shine ya bada wannan sanarwa a karshen taron Majalisar Ministoci a ranar Talata da yamma.
Yace a ranar 21 ga watan Fabrairun shekara ta dubu biyu da goma sha shidda za'a yi zaben shugaban kasa dana wakilan Majalisar dokokin kasar.
Alhaji Dudu Rahman mai magana da yawun jam'iyar masu hamaiya yace sun yi mamakin wannan sanarwa ta gwamnati. To amma yace dama talakawan Niger sun dawo daga rakiyar gwamnati, kuma tana tsoron masu hamaiya zasu kada ita a zabe.
Yace sanarwar ba bisa ka'ida ba.,
Ita kuma gwamnatin Niger, ta danganta korafe korafen masu hamaiya da rashin shirin yin zabe.