Sa'adu Muhammad daya daga cikin daliban da matsalar ta rutsa dasu yace hukumar jami'ar ta bukaci agwamnati ta rubuto takardar daukan alkawarin biyan kudaden daliban amma shiru kake ji.
Sa'adu yace abun da ya daure masu kai yanzu shi ne basu sani ba ko an sanarda gwamnatin ko ba'a sanarda ita ba. Saboda haka suna cikin wani mawuyacin hali. Kawo yanzu sun yi wata hudu babu karatu babu kudin makaranta.
Bayan watanni hudu na zaman kashe wando da daliban suka yi matsaloli sun fara dabaibaye rayuwarsu. Jamilu Abubakar yace wadanda suka fara karatun tare sun gama jarabawa har ma yanzu suna maganar tafiya hutu. Banda rashin karatu abincin da suke dashi ya kare.
A cewar daliban binciken da suka gudanar ya tabbatar cewa gwamnatin jihar Sokoto ta biya dan barandan duk wani kudi da daliban ke bukata. Binciken ya nuna akwai alama rijiya ta bada ruwa guga ta hana; ma'ana gwamnati ta biya kudin amma dan baranda ya danne.
Dan barandan ko wakilin daliban wai yana Sokoto.
Kafin daliban su taso daga Sokoto an shaida masu cewa karatunsu zai dauki shekaru hudu. Gwamnatin jihar Sokoton ita ce zata biya kudin makaranta da kudin shansu da cinsu na tsawon shekaru hudu.
Watanni biyu da suka gabata gwamnati ta yi bincike amma har yanzu babu wani abu da ya fito.
A can baya daliban sun ce ofishin jakadancin Najeriya ya taimaka masu da wasu kudi.
Ga karin bayani.