Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da nadin Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a matsayin sabon sarkin masarautar Ningi na 16 a kan mataki, Sarki mai daraja ta 1.
“Muna tuhumar su da aikata laifuka da suka hada da tada hankali da jiwa jama’a ko jami’ai rauni ko lalata dukiya,” in ji CP Auwal.
Mabiya Addinin Kirista Iklisiyyar United Methodist Church a Najeriya, sun gudanar da zanga zanga ta lumana don nuna kyama ga batun auren jinsi da wassu Shugabannin Iklisiyar Methodist Church ke kokarin ganin mabiyan sun amince dashi.
Al ‘ummar yankin karamar hukumar Nafada a Jihar Gombe suna fuskantat wani yanayi mai tsoro da fargaba sakamakon bullar wata cuta da ta lakume rayukan yara da matasa sama da talatin.
A watan Fabrairun da mu ke ciki ne ake sa ran za a fara tonon albarkatun man fetur da iskar gas da aka samu a Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Babban Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya bada gudummawar kudi Naira Miliyon dari (100) domin Taimaka wa Mutanen kasar Falasdinu da suke yaki da kasar Israila.
Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar da dan takarar APC Abubakar ya shigar wacce ke kalubalantar nasarar gwamnan na Bauchi.
Rahotanni daga Najeriya na bayanin cewa, babban bankin kasar, wato Central Bank Of Nigeria (CBN), ya rufe bankuna guda 754 da suka hada da manya da matsakaita da kuma bankunan sayen gidaje a fadin kasar, sakamakon matsalolin da bankunan suka shiga.
Jami’an tsaro na farin kayan sun kama matasan samari maza kimanin 76 a lokacin da suka taru a wani katafaren wajen shakatawa mai suna Duwa Plaza a garin Gombe, da zimmar gudanar da bikin zagayowar shekarar haihuwan daya daga cikinsu.
Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya, na nuni da cewa wasu mutane 39 ‘yan asalin Duguri da ke yankin karamar hukumar Alkaleri da ‘yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da ta gabata, a wani aikin sintiri na hadin gwiwar Jami’an tsaro da mafarauta.
Gwamnonin Jihohin shiyyar Arewa maso Gabas sun gudanar da taron Kungiyar na Takwas inda suka bukaci gwamnonin jihohin su tabbatar an bi dokokin yin amfani da dokar kasa da aka tanadar wajen harkar ma’adinai ta hanyar da aka amince.
Ayyukan ta’addanci a shiyar Arewa Maso Gabascin Najeriya, musamman sace sace mutane don neman kudin fansa yana ci gaba da samun gindin zama.
Matsalar ‘yan bindiga dake kaddamar da hare-hare da kuma satan mutane don neman kudin fansa a jihar Bauchi na ci gaba da ta’azzara.
Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta tashin haikan wajen ceto matasan jihar daga matsalolin kayan maye da ayyukan daba, ta wajen hada kai da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.
A halin da ake ciki, Zlatan Ibrahimović ya ayyana yin ritaya daga wasan kwallon kafa na kwararru, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da magoya bayan klub din AC Milan a karshen wasan da suka yi da klub din Hellas Verona a San Siro
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Abdulkadir Muhammad (Kauran Bauchi), wanda tauraruwarsa ke dada haskakawa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ma siyasar kasar baki daya, ya dada yin fice bayan da gwamnonin jihohin Najeriya da ke karkashin mulkin PDP su ka amince ya jagorance su.
An mika tubabbun yan Boko Haram 12 ga iyayensu a bayan da suka shafe shekaru 14 a sansanonin daidaita lamarinsu, an gudanar da bikin mika su ne a ofishin hukumar addini ta jihar Bauchi, wanda ya samu halartar yan uwan tubabbun yan Boko haram din.
Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Super Falcons a Najeriya tana taka rawar gani a fafutukar da take yi don tunkarar gasar cin kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a kasashen Australia da New Zealand kasa da kwanaki dari.
Domin Kari