Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty International Na Fuskantar Barazana Daga Sojojin Najeriya


Tambarin kungiyar Amnesty International
Tambarin kungiyar Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce tana fuskantar barazana daga rundunar sojojin Najeriya bisa yadda take gudanar da aikinta na ba sani ba sabo.

Amnesty International ta ce rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da yi mata barazana da kokarin tsoratar da ita da zummar ta watsar da hakikanin sakamakon binciken danne hakkin bil Adama da kungiyar ta ce sojojin na gudanarwa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ta ce ranar 24 ga watan Mayu ta bayar da rahotan yadda sojoji ke aikata lalata da mata ‘yan gudun hijira kafin a basu abinci, al’amarin da Amnesty ta ce sojojin sun fusata kwarai inda suka fara batawa kungiyar suna da yi mata barazana.

Maimakon rundunar sojan Najeriya ta dauki matakan gyara kan zargin fyade da sauran laifukan yaki da dakarunta ke yi, amma sai suka ci gaba da karyata wannan zargi.

Ita dai kungiyar Amnesty ta ce aikace-aikacenta ba ya tsaya bane kadai ga tattara bayanai kan take hakkin bil Adama da soji ke yi a kasar, amma sun sha yin magana kan muguntar Boko Haram ga fararen hula da kuma yadda ‘yan sandan Najeriya ke cin zarafin jama’a.

Kakakin kungiyar Amnesty International a Najeriya, ya bayyana cewa ba suna gudanar da aikinsu bane domin su bakantawa sojojin ba, domin babu wani abu da zasu karu da shi don sun bakantawa sojojin.

Ita kuma hedikwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da kalaman da kungiyar Amnesty ta yi, inda suka kira kungiyar a matsayin makiyar Najeriya, kuma wadda bata son zaman lafiya a kasar.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG