Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ba Najeriya Tallafin Dala Miliyan 102


Jakadan Amurkaa Najeriya Mr. Stuart Symington a yayin da yake bayyana gudunmuwar Dala miliyan $102 da Amurka ta baiwa Najeriya
Jakadan Amurkaa Najeriya Mr. Stuart Symington a yayin da yake bayyana gudunmuwar Dala miliyan $102 da Amurka ta baiwa Najeriya

Gwamnatin Amurka ta bai wa Najeriya taimakon dala miliyan dari da biyu domin a ci gaba da agazawa mutanen da rikicin Boko Haram ta rutsa da su a yankin Arewa maso gabas.

Da yake bayyana tallafin yau a Abuja, Jakadan Amurka a Najeriya, Ambassada Stuart Symington, ya ce karin tallafin na dala miliyan dari da biyu ($102 M) na aikace-aikacen jinkai ne a yankin arewa maso gabas inda za a samar da matsugunni, da kiwon lafiya, da abinci da kuma tsaro ga al'ummar yankin.

Wannan tallafi na daga cikin adadin dala miliyan dari da goma sha biyu ne da Amurka ta kebe don taimakon yankin Tafkin Chadi.

Amurka tace tana fata wannan karin taimakon ya zama silar yin aiki tare da gwamnatoci domin samun dauwamammen zaman lafiya da lumana a yankin,

Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin mutane da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Kuma kawo yanzu, Amurka ce ke kan gaba wajen bada tallafi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG