Yanzu haka wata matsalar dake addabar jama’a dake tsakanin jihar Taraba da Binuwai ita ce ta garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.
Baya ga sace wani hakimi da aka yi cikin kwanakin nan a jihar Taraba wanda daga baya aka maido da shi bayan an biya wasu kudade, sai kuma wanda ya sake faruwa a jiya Alhamis na sace wani dan kasuwa kuma dattijo a garin Zaki-Biam, Alhaji Munkaila Zaki Biam, lamarin da ya jefa al’umman wadannan yankuna cikin halin zulumi da fargaba.
Ganin yadda lamarin ke kara kazanta ne,yasa al’ummomin wadannan yankuna kiran da akai musu dauki.
A cewar wani ganau, da misalin karfe takwas ne wasu suka isa shagonsa inda yake zaune da wani abokinsa suka daukeshi sai cikin motarsu kana suka yi tafiyarsu. Har yanzy babu duriyarsa. Mai maganan ya ce yanzu suna cikin dimuwa kwarai saboda wanda aka sacen dan kasuwa ne da ya yi fiye da shekaru hamsin a garin.
A kullum dai hukumomin tsaro cewa suke suna nasu kokari don gano bata garin ke aikata wannan mummunan aiki.
ASP David Misal dake zama kakakin rundunan yan sandan jihar Taraba,wanda ya tabbatar da sako hakimin da aka sacen a Taraba,ya bayyana irin matakan da suke dauka tare da kiran al’umma su dinga basu bayaai akan bata garin da suka sani dake tsakaninsu. Idan kuma suna neman kudin fansa ya kira jama’a su basu bayanai domin su ‘yan sanda su yi aikinsu yadda ya dace.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum