Babbar Kotu a Ivory Coast ta ayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa da aka gudanar bara, wanda hakan warware maganar da ta yi a baya c eta goyon bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo.
A jiya Alhmais, Kotun Kundin Tsarin Mulki ta tabbatar da sakamakon zaben da hukumar zabe ta gabatar mai nuna cewa shugaba Ouattara ya ci zaben da kashi 54 cikin dare na kuri’un da aka kada.
Kotun ta yi watsi da sakamako a can baya a watan Disamba. A maimakon hakan sai ta soke kusan kashi 10 cikin dari na kuri’un da sunan wai na magudi ne ta kuma ayyana Mr. Gbagbo a matsayin wanda ya ci zaben da kashi 51 cikin dari na kuri’un da aka kada.
Mr. Gbagbon dai ya yi amfani da wannan ayyanawar wajen darewa kan gadon mulki. Kin mika ragamar ikon day a yi ya haddasa tashin hankali, da jayayyar shugabanci na tsawon wata hudu wanda hakan ya yi sanadin mutuwar daruruwar mutane da kuma kimanin wasu miliyan guda da su ka rasa muhallansu.
A wata sabuwar kuma a jiya Alhamis, Amurka ta ce za ta samar da kudi wajen dala miliyan 8.5 don agaza wa ‘yan Liberiyan da su ka guje daga muhallansu a lokacin yamutsin. Jami’an gwamnatin Amurka sun ce za a yi amfani da kudin wajen samar da kayan magunguna, da tsabtataccen ruwa da sauran muhimman kayan gida.