Jami’an binciken dake aiki tare da jami’an ofishin kare hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ran litinin, suka bayyana cewar sun gano kabarurrukan mutanen ne a Unguwannin dake wajen birnin Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast. Mazuna unguwannin sun bada shaidarcewa gawarwakin da aka gani na wadanda aka kashe ne a ran 12 ga watan Afrilun da ya gabata lokacin da ‘yan bindiga dake goyon bayan hambararren shugaba Laurent Gbagbo suka kaiwa masu goyon bayan sabon shugaba Ouattara hare-hare domin tsoratasu.
Jami’an hukumar kare hakkin Bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya sun bada sanarwar cewa sun fara gudanar da binciken rahotannin da aka bayar dake cewa an gano wasu kabarurruka a yashe a unguwannin Yopougon, ana kuma kyautata cewar gawarwakin farar hular da aka yiwa kisan gilla da ake zargin sassan biyu dake gaba da juna da aikatawa.