Amurka na nuna damuwarta da yadda ake ta girke askarawa a yankin Abyei na Sudan da ake takaddama a kai.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner, ya fadi cewa Amurka ta yi tir da girke mayaka a bangarorin biyu. Ya ce wannan fito-na-fito ne mai hadari kuma ba abin yadda ba ne.
Kakakin yace tabarbarewar al’amura a yankin zai kawo nakasu ga yarjajjeniyar zaman lafiyar da kasar ta cimma a 2005.
A farkon wannan satin, sojoji daga bangarorin arewa da gudu sun gwabza a yankin na Abyei, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 14. Arewaci da kudancin Sudan sun sha zargin juna da tura dinbin sojoji a yankin na Abyei.
Yankin na Abyei mai arzikin man fetur ya kasance fagen daga a yakin basasar Sudan na tsawon shekaru 21.
Kudancin Sudan ya kada kuri’ar bukatar ballewa daga arewaci da gagarimin rinjaye a kuri’ar raba gardamar da aka gudanar a watan Janairu, wadda shugabannin bangaren arewa su ka ce za su mutunta. To saidai fa har yanzu ba a tantance makomar yankin na Abyei ba.