Mai gabatar da kararraki na kasar Ivory Coast ya ce a yau lahadi zai tinkari matar tsohon shugaba Laurent Gbagbo da tambnayoyi a garin Odienne. Simone Gbagbo ta taka rawa sosai a cikin harkokin gwamnatin mijinta.
Ana binciken Mr. Gbagbo da dakarun tsaronsa dangane da irin rawar da suka taka a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben watan Nuwambar bara, inda aka kashe daruruwan mutane.
Masu gabatar da kararraki a karkashin jagorancin Simplice Kouadio Koffi, sun yi ma tsohon shugaba Gbagbo tambayoyi jiya asabar ba tare da lauyoyinsa Faransawa ba, wadanda suka isa birnin Abidjan amma aka hana su shiga cikin kasar. Jami’an gwamnatin Ivory Coast suka ce lauyoyin ba su da bizar shiga cikin kasar.
A ranar jumma’a aka rantsar da abokin adawar Mr. Gbagbo, Alassane Ouattara, a matsayin shugaban kasa. Mr. Ouattara ya karbi ragamar shugabancin kasar a watan da ya shige a bayan da magoya bayansa, tare da taimakon sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya, suka kama Mr. Gbagbo da matar ta sa a gidan shugaban kasar.