Yanzu haka wasu Jami'an kasar Koriya ta Kudu biyu suna kan hanyarsu ta zuwa Amurka domin yiwa jami'an gwamnatin Amurka bayani kan tattaunawarsu da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.
Chung Eui-yong, shugaban hukumar tsaro ya bar birnin Seoul yau Alhamis tare da shugaban hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu, Suh Hoon. Ana sa ran Chung da Suh zasu tattauna kan ganawar da suka yi cikin makon nan da shugaba Kim a Pyongyang da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson da mai baiwa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaron kasa H.R. McMaster.
A cewar Chung Eui-yong, shugaban Koriya ta Arewa yayi tayin soke shirin gwajin makamansa na nukiliya da masu linzami, yayin da kasar ta hau teburin sulhu da Amurka kuma aka tabbatar mata da tsaron kasarta.
Da yake magana da manema labarai yau Alhamis a birnin Addis Ababa, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Amurka na bukatar tabbtar da gaskiyar lamarin akan zaman tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Facebook Forum