Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yamutsin Fadar White House Ya Yi Sanadin Faduwar Kasuwannin Hannun Jari


Gary Cohn wanda ya yi murabus saboda karin haraji kan tama da karafan dake shigowa daga waje da Shugaba Trump ya hakikance sai ya aiwatar
Gary Cohn wanda ya yi murabus saboda karin haraji kan tama da karafan dake shigowa daga waje da Shugaba Trump ya hakikance sai ya aiwatar

Murabus din da mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin tattalin arziki biyo bayan rashin jittuwarsu akan dagewar shugaban na kara haraji akan karafa da tama dake shigowa daga kasashen waje ya haifar da faduwar kasuwannin hannun jari kamadaga Amurka zuwa kasashen Asiya

A halin da ake ciki kuma, fargabar da ta kunno kai a game da yiwuwar sa-in-sar cinikayya ta sa wadansu kasuwannin hannayen jarin Amurka da na kasashen Asiya faduwa jiya Laraba, biyo bayan murabus din mai ba shugaban Amurka shawarwari kan harkokin tattalin arziki.

Darektan majalisar harkokin tattalin arziki ta kasa, Gary Cohn, yana kan gaba wajen yin adawa da shirin shugaba Trump na kara kudin fito da kashi 25 kan Tama, da kuma kashi 10 cikin 100 a kan goran ruwa, ko farin karfe, da ake shigowa da su Amurka daga wasu kasashe.

A lokacin da yake jawabin bayyana murabus dinsa, Cohn ya ce “Na gode da damar da aka bani in bautawa kasata, na kuma gabatar da wadansu tsare tsaren da zasu amfani Amurkawa, musamman yin garambawul ga tsarin haraji na tarihi."

A hada-hadar da aka yi jiya a kasuwannin hannayen jari, alkaluman Dow Jones dake auna darajar masana'antu 30 mafiya girma a Amurka, sun fadi da kimanin kashi daya cikin 100 a lokacin bude kasuwa, amma daga bisani suka farfado, aka rufe kasuwa su na kasa da kimanin sulusin kashi daya. Alkaluman S&P sun fadi kasa kadan, a yayin da alkaluman kamfanonin fasaha na NASDAQ suka cira sama tare da muhimman alkaluman hannayen jari na kasashen Turai.

Tun farko a Asiya, alkaluman kasuwar hannayen jarin Hong Kong ta Hang Seng sun yi kasa da kashi 1 cikin 100, yayin da hannayen jarin Nikkei na kasar Japan suka fadi da kadan.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG