Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Zata Wargaza Shirin Nukiliyar Ta


Kim Jong Un
Kim Jong Un

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Popmpeo yayi maraba da "muhimman alkawuran" da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un yayi, a wani taron koli da sukayi da takwaran aikinsa na Koriya ta Kudu.Koriya ta Arewa ta bayyana cewa cewa zata wargaza tashar gwaje gwajen makaman Nukiliyarta karkashin wata yarjejeniya ta musamman da suka yi tsakanin shugabannin yankunan Koriyan biyu.


Pompeo ya bayyana a jiya laraba cewa ya gayyaci ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa Ri Yong Ho, da su gana a birnin New York, a lokacin da za'a yi babban taron zauren majalisar dinkin duniya. Ya kuma kara da cewa an gayyaci wakilan hukummin kasar da suke Pyongyang da su gana da manzon Amurka na musamman kan Koriya ta Arewa a birnin Austria, idan suka sami dama nan bada jumawa ba.


Shugaba Trump ma yayi murna da labarin da yaji daga Koriya ta Arewa bayan taron kolin, ya kuma shaida wa manema labarai a fadar White House.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG