A samamen da suka kai a kasuwar Kato da tashar shiga motocin haya da aka fi sani da tashar Kollo dake Yamai ‘yan sandan farin kaya da hadin gwuiwar hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi OCRITIS suka yi wannan babban kamu da ya kumshi wasu dilalai dauke da dimbin tabar wiwi da miyagun kawoyoyi irinsu TRAMADHOL ( TRAMOL) wadanda aka gabatar da su gaban ‘yan jarida.
Nazirou Moussa Boubakar kakakin hukumar ‘yan sanda ya ce tare da hadin kan wasu jami’an tsaro suka kai samamen da ya basu nasarar capke bata garin wajen su 108. 83 daga cikin wadanda aka kama, an kamasu ne da laifin sha da sayar da kwaya. Sun kama kanabis da makamantansu kamar tramol 3415.
Hukumar ‘yan sandan ta kara da cewa ta kama motar Taxi a hannun ‘yan durba durba hade da wasu baburan da ake yiwa kallon na sata ne.
Tabarbarewar al’amuran tsaro a birnin Yamai wani abu ne da ke matukar tayarda hankalin jama’a. Hakan na faruwa ne bisa la’akari da yadda ‘yan fashi suka mayarda kisan kai tamkar wani abu mai sauki lamarin da ake alakantawa da yawaitar amfani da myagun kwayoyi
A saboda haka, hukumar ‘yan sanda ta nemi hadin kan kwamitin tsaron yankin Yamai don takawa wannan matsala burki.
A saurari rahoton Souley Mummuni Barma
Facebook Forum