Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakacin Jami’an Tsaro Ne Ya Sa Boko Haram Ke Yawan Kai Hare-hare


Janar Tukur Buratai sojoji yayinda suka shiga cikin dajin Sambisa
Janar Tukur Buratai sojoji yayinda suka shiga cikin dajin Sambisa

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin arewa maso gabashin Nigeria ya yi Allah-wadai da kisan da aka yiwa wata jami’ar kungiyar agaji ta Red Cross a yankin, Saifuna Hussaini Ahmed Khorsa, bayan sun yi garkuwa da ita tun a watan mayu da ya gabata.

Masana harkokin tsaro na cewa, kara dagulewar yanayin tsaro a yankin arewa maso gabashin Nigeria ba ya rasa nasaba da sakaci daga bangaren jami’an tsaro, kamar yadda wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Nigeria, Manjo Hassan Abdul’aziz mai ritaya ya fadi.

Yace shigar ‘yan Boko Haram sannanin ‘yan gudun hijira dake Rann abun mamaki ne, domin ya kamata sansanin na da tsaro fiye da tsammani da zai hana kowane irin hari da za’a kawo. Amma ‘yan ta’addan sun shiga sansanin har suka sace mutane da yanzu wata shida ke nan suna rike dasu. Gwamnatin Nigeria da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da suke yiwa aiki ba su yi komi ba har yanzu ‘yan ta’addan sun soma kashesu.

Mano Hassan Abdulaziz ya ce ba cin kasa ba ne abu riketa shi yake da mahimmanci. Sojojin Nigeria na ikirarin murkushe ‘yan Boko Haram amma bas u rike wuraren da suka kama daga ‘yan ta’addan. Bayan a tarwatsasu suna dawowa su sake haduwa su ci gaba da kai hare hare domin sub a sojojin Nigeria kunya.

Manjo Hassan ya ce sakacin sojojin ya say an Boko Haram kutsawa sansanin. Kamata ya yi ko kuda ne zai shiga wurin sojoji su kare saboda a lokacin wurin ya kunshi mutane fiye da 150,000.

Yace yankin arewa maso gabas ya koma gidan jiya saboda sojoji ba su yi abun da ya kamata su yi ba. Da sun ci gaba da kai masu samame, su hanasu sakat da ba su iya sake taruwa wuri guda ba. Baicin hakan duk wata hanya da aka sani suna samun kaya da sai a toshe, su kuma lura da baragurbi da ana iya samu ko a cikin sojojin ko kuma sojojin hadaka ko cikin fararen hula ma.

A saurari hirar da Manjo Hassan ya yi da Mahmud Kwari

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG