Korea ta arewa ta yi watsi da gargadin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata na cewa zai dauki matakin soji akan kasar, idan har ta ci gaba da yi wa Amurkan barazana.
A ranar Talatar da ta gabata shugaba Trump ya shammaci masu adawa da shi da magoya bayansa a gida da waje, tare da shan alwashin kai hari akan Korea ta arewa, inda ya yi amfani da zafafaan kalamai da wasu ke suka.
Trump ya bayyana cewa kasar ta Korea ta arewa za ta fuskanci "ukubu da luguden wuta," muddin ba ta fita hanyar Amurka ba.
Sai dai Janar Kim Rak Gyom, wanda shi ne kwamandan tsare-tsare na rundunar da ke sarrafa makaman roka, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Korea ta arewa na KCNA a yau Alhamis cewa, kalaman na Trump duk ashana ne, domin ba abinda zai iya aiwatarwa ba ne.
A jiya Laraba, sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya ce Korea ta arewa na iya fuskantar barazanar a daidaita ta, idan har ta haddasa yaki, ya kuma yi kira ga hukumomin kasar da su yi watsi da shirinsu na mallakar makamin nukiliya.
Facebook Forum