Manyan jami'an hukumomin leken asirin Amurka sun ki su sassauta damuwa da suke nunawa dangane da kasar Rasha, yayinda shugaban Amurka Donald Trump da jami'an Rasha suke bayyana damuwa kan tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen biyu.
"Manufofi da al'adun mu sun yi karo da juna, " inji darektan hukumar leken asiri karkashin ma'aikatar tsaro Leftanar Janar Vincent Stewart, yayinda yake magana da wasu manema labarai.
Stewart, wand a yayi magana gabannin barkewar sabuwar cacar baki tsakanin shugaba Trump da wakilan majalisun Amurka kan batun na Rasha, ya kuma yi gargadin cewa Moscow tana da zarafin yin katsalandan kuma ta shirya farfagandar da zata biya mata bukata.
A cikin makon nan ne shugaba Trump ya sanya hanu kan sabbin takunkumi da majalisun dokokin kasar biyu suka amince da gagarumar rinjaye. Nan da nan ya hau Twitter yayi zargin cewa danganatak tsakanin kasashen biyu ya tabarbare ainun, amma ya za laifin hakan kan majalisun dokokin kasar.
Facebook Forum