Sabuwar kididdigar jin ra’ayin jama’a da aka yi a nan Amurka ta nuna cewa farin jinin shugaba Donald Trump, wanda shi ne wanda yafi bakin jini fiye da dukkan shugabanin da aka yi a farkon wataninnsu akan mulki, ya na ci gaba da raguwa.
Jiya Laraba jami’ar Quinnipiac ta fada cewa kimanin kashi 61 cikin 100 na Amurkawan da aka nemi ra’ayinsu, ba sa goyon bayan manufofi da take-taken shugaban na Amurka, yayin da kashi 33 suka nuna akasin hakan.
An yi kiddigar ce cikin ‘yan kwanakin da suka shige, lokacin da Fadar White House ke fama da matsaloli.
A lokacin da ake jin wannan ra’ayi ne, shugaba Trump ya kori shugaban ma’aikatan fadarsa Reince Priebus da kuma darektan sadarwa Anthony Scaramucci, yayin da kuma Majalisar dattijai ta yi watsi da shirin soke dokar kiwon lafiya, sokewar da shugaba Trump yake goyon baya.
Shekaru bakwai da suka gabata tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya rattabawa dokar hannu wacce ake wa lakabi da Obamacare.
Facebook Forum