Amurkawa sun jira zuwa yau Alhamis su ga ko kirgen kuri'un wasu jihohi da dan sama zai kai ga sanin tartibin wanda ya ci zaben shugaban kasa, kwana guda bayan nasarar lashe jihohi biyu masu muhimmanci ta sa tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kusa da nasara, inda kwamitin yakin neman zaben shugaba kasa Donald Trump kuma ya shigar da jerin kararraki.
Har yanzu dai kafofin yada labaran Amurka ba su yi hasashen wanda ya lashe jihohi shida da suka hada da Alaska, Arizona, Georgia, Nevada, North Carolina da kuma Pennsylvania ba.
Hasashen jiya Laraba ya saka Biden a matsayin wanda ya yi nasara a jihohin Michigan da Wisconsin, jihohi biyu da Trump ya lashe a zaben 2016.
“Ba wai nazo nan ne na bayyana cewa mun lashe zabe ba. Amma na zo nan nedon na baku rahoto cewa idan aka kammala kidayar kuru’u, munyi imanin mu zamu lashe,” abin da Biden ya bayyana kenan jiya Laraba da rana.
Biden na iya samun kason kuru’un zabe 270 da ake bukata don lashe zabe idan ya cigaba da zama kan gaba a jihohin Nevada da Arizona.
A tsarin zabe irin na cin kason kuri'u a Amurka, wanda ya samu kuru’u mafi yawa a kowace jiha, idan ban da jihohi biyu Maine da Nebraska, shi yake samun duk kason kuri'un jaha, wanda ake rabawa kan yawan jama’ar jihar.
Facebook Forum